Thursday, 24 May 2018

Ragwaye Ne Masu Kukan Yunwa A Gwamnatin Buhari, Cewar Shugaban Kwastan Hameed Ali

Ragwaye Ne Masu Kukan Yunwa A Gwamnatin Buhari, Cewar Shugaban Kwastan Hameed Ali

Shugaban hukumar Kwastam ta Nijeriya Hameed Ali ya ce mafi akasarin ‘yan Nijeriya da ke kukan yunwa a karkashin gwamnatin shugaba Buhari ragwaye ne da basu da karfin zuciyar tashi domin neman na kansu.

Shugaban na Kwastam ya bayyana haka ne, yayin da ake karin haske dangane da nasarorin shirin gwamnatin Najeriya akan bunkasa ayyukan noma a kasar, a wata ganawada yayi da kungiyar magoya bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja.

A cewar Hameed Ali, babu yadda za ayi abinci ya rika fadowa mutane daga sama, dan haka ya zama tilas mutane su tashi tsaye domin amfani da damarsu wajen neman abin rufawa kai asiri.

Dangane da shugabancin Buhari kuwa, shugaban na kwastam ya ce kaunar Najeriya da ‘yan kasar ne ya sanya shi fafutukar karbar jagorancin kasar duk da cewa shekarunsa sun haura 70.

Ali ya kara da cewa inda shi ne ya ke da yawan shekarun shugaba Buhari, ga fansho mai kyau da gidansa na zama a Daura, ba zai dorawa kansa nauyin da zai hanashi sararawa ba ta hanyar shiga siyasa, amma kaunar kasarsa ta sa shugaba mai ci yanke shawarar.

No comments:

Post a Comment