Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa duk wanda aka samu ya aurar da diya mace da bata balaga ba wato bata shekara 18 ba laifi ne kuma duk wanda gwamnati ta kama da aikata hakan zai fuskanci fushin hukuma.
Gwamnan jihar, Kashim Shettima ne ya yi wannan gargadi a ranar Laraba yayin ya ke jawabi ga iyayen yara da ke amfana da shirin samar da ilimi kyauta ga yara da gwamnatin jihar ta kaddamar.
Gwamnatin jihar kuma ta bawa iyayen yaran kyaututuka wanda suka hada da kayayakin abinci, tufafi don kara musu gwarin gwiwa na tura yaransu mata zuwa makaranta a maimakon aurar da su tun kafin su girma.
Shettima ya ce: "Ku kyalesu su kammala karatun sakandare, ko mun baku taimako ko bamu baku ba, duk wanda aka kama ya aurar da diyarsa mai shekaru 12 zai fuskanci hukunci.
"A matsayinmu na iyaye, ya zama dole mu taimakesu su samu ilimin boko da addinin musulunci," inji gwamnan.
Mafi akasarin fulanin da ke zaune a garin yan gudun hijira ne wanda suka baro gidajensu a yankin tafkin Chadi. Kafin gwamnati ta kaddamar da samar da ilimin kyauta, mafi yawancin fulanin basu tura yaransu makarantar boko.
Sai dai a yanzu, gwamnatin ta wayar da kansu game da fa'idojin da ke tattare da ilimin boko musamman ga yaransu mata.
A kalla yaran fulani 600 neke amfana daga shirin bayar da ilimi kyautar.
A cewar gwamnatin jihar, za'a samar wa fulanin da suka rasa muhallinsu gidajen da za su zauna.
Ana sa ran za'a ware gidaje 100 daga cikin wanda attajirin dan kasuwa Aliko Dangote ya gina a matsayin gudunmawarsa ga wadanda rikicin ta'addanci ya ritsa da su.
No comments:
Post a Comment