Shugaba Muhammadu Buhari ya soke kwangilar nan ta sake sayo kayan tsaro, wadda ministocin sa suka kirkiro, saboda zargin harkalla a cikin kwangilar.
Kwangilar wadda Ministocin suka sa wa hannun a cikin watan Disamba, 2017, an rattaba cewa za a bai wa kamfanin kwangilar mai suna HSLi zungurutun kudi har dala milyan 195, shi kuma zai kawo jiragen yaki da helikwafta da kuma jirage kanana na yaki na ruwa, 12 daga Isra’ila.
An ce Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ne ya shirya kwangilar, yayin da masu sukar lamarin suka ce an kirkiri kwangilar ne domin a saci kudade kawai.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari ne ya rubuta wa Antoni Janar na Najeriya, Abubakar Malami wasika cewa a soke kwangilar.
Sannan kuma Buhari ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da kuma hukumar liken asiri ta kasa da su binciki yadda kamfanin ya samu yarjewar yin kwangilar ba tare da samun satifiket na gangariyar amincewa da tabbacin ko sahihancin yay i kwangila a kasar Isra’ila ba.
Sannan kuma Buhari ya bada umarnin cewa kamfanin kwangilar ya kawo kayayyaki na dala miliyan 50, wato na adadin kudin da aka fara ba shi a matsayin somin-tabi tun kafin ya fara kawo komai.
Binciken da Arewa Dailypost ta gudanar ya nuna cewa kamfanin HSLi ba shi ma da rajista a kasar Isra’ila, amma sai ya hada baki da wani kamfani na kasar Isra’la mai suna Mitrelli, wanda aka ce kamfanin ya na da alaka ta kusanci da Minista Ameachi.
Cikin 2012 a lokacin da Ameachi ke gwamnan jihar Rivers, ya taba bai wa Mitrelli kwangilar aikin wata gona a can gefen Fatakwal har ta tsabar kudi dala milyan 140.
A da can babu ruwan Mitrelli da harkar makamai, amma a dare daya kamfanin ya tsoma kan sa a cikin kwangilar makamai.
No comments:
Post a Comment