.... Gwamnan Bauchi ya amince da karin albashin ma'aikatan kiwon lafiya a jihar
"Kamar yadda na baiyana a cikin takardar bari na aiki, na ajiye aikina ne don bisa ra'ayina. Ina kira ga al'ummar jihar Bauchi da su rungumi gwamnatin jihar Bauchi domin cigaban jiha.
"Ban ajiye aiki na don wata manufa ba, kawai na ajiye aikina ne kasancewar na kudiri aniyar wa'adi daya zanyi akan kujerar mukaddashin gwamnan jihar Bauchi.
"Ban ajiye mukamina don tozarta gwamnati ba kamar yadda wasu ke fassara hakan, na ajiye mukamina ne kawai don kaina kuma har gobe ina tare da gwamnatin jihar Bauchi. Ina kira ga dukkan maison cigaban jihar Bauchi da ya marawa gwamnati baya domin cigaba da aiyukan alkairi wa jihar Bauchi", mamar yadda Injiniya Gidado ya bayyana.
A gefe daya kuma, Gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Mohammed A. Abubakar, ta amince da biyan ma'aikatan kiwon lafiya albashin su na tsarin nan na ma'aikatan kiwon lafiya, a jihar Bauchi.
Gwamna M.A ya amince da biyan wannan kudi kaso dari cikin dari da ma'aikatan suka jima suna neman a aiwatar musu da shi na tsarin nan na (CONMESS) da kuma na tsarin (CONHESS) na ma'aikatan kiwon lafiya na jihar bauchi
Wannan sanarwan karin data fara aiki ne a wannan wata na mayu na shekaran 2018
Mai tallafawa Gwamnan jihar Bauchi akan harkokin sadarwa Alhaji Shamsuddeen Lukman Abubakar shine ya shaidawa manema labarai hakan.
No comments:
Post a Comment