Wednesday, 15 June 2016

Halaccin Sarauta episode 24


Previous episodes of Halaccin Sarauta episode 24

Continuation of Halaccin Sarauta episode 25

Gabanta fadi yake don babu irin tunanin dabatayi ko wanene ba, dahaka suka isa fada taga bayanda tasaba ganin mutane ba, andan cika sosai, fannin falmata aka nufa da ita inda taana ganinta ta taso ta wanka mata mari umma uwar soro ne tayi sauri taja aliya wacce tarike kuncinta cike da takaicin abunda yasameta batasan metayi ba ankafamata mari, falmata cikin fushi take cewa "duk wanda ke da hannu acikin wannan aikin kuhado min dashi," ahanyan fita da itane taga sufyan da abdullahi suna tsaye ganinta da yayi yasa ya tsure anma bai gwadaba don kar wani ya tsammace wani abu, yaja abdulllahi gefe tare da tambayanshi meya faru? "Kasan harkan mata da matsala, nagayawa yusuf yabar yarinyannan saboda abunda zai jawo mata, mahaifiyarsa batada shariya, yaki yadda, yanzu yazo yakwanta ciwo tun ast week, anma ciwon yayi tsanani ne shekaranjiya wanda dogaransa sunce daya dawo daga gidan aliya ne yakwanta. Kuma sumbatu yake yana kiran sunanta, hakan yasa mahaifiyar tace ko aliya tamishi wani abune, wai mayya ce tanason cinye mata da, " "Subhanallah" "Yanzu dole munemi hanyar fidda aliya daga wannan matsifan narasa meya dawo da ita garinnan" "Muje muga gimbiya" Suka nufi fannin gimbiya yakolo inda suka mata bayanin abunda ke faruwa hankalinta yatashi sosai, anma babu yadda ta iya bata isa tasaka baki aciki ba, don baa haka, yazama dole tanemi mai ceton aliya hakan yasa tafito don zuwa ganin aliya wanda akasa a cage, aliya idonta ya kumbura yayi bul don tasha kuka, ita badamuwanta abunda suke mataba damuwanta shine yusuf yawarke ko zata gwada masa irin son datake mar, kodataga gimbiya tuni kukan yakaru,gimbiya ta yi umurni wa masu gadin dasu fice zatayi magana da ita suna fita tariko hannunta "Aliya meya faru? Kigayamin gaskiyan abunda kika sani" Cikin kuka aliya tabata labarin abunda yafara faruwa tundaga tsohon gidanta, zuwa haduwanta dasu hassana da hussiena dazuwamshi data koreshi da ilya, dakuma zuwanshi na biyu shekaranjiya kenan sannan tacigaba dacewa "wlh ranki shi dade ni ba mayya bace,jinina a tsarkake yake," Gimbiya yakolo taji tausayinta anma babu yadda ta iya donhaka tace "bazai yiwu naceceki ba, dole dole shi zai ceceki idan yamike akan gado, inhar bai mike ba, zata iyasakawa a illata ki"hankalin aliya yakara tashi bata taba jin mutuwa zamzam haka ba, tagama tsorata tarasa ina zata saka ranta, gimbiya tasamu tadan lallabata kafin takoma fanninta ta ai akira bilki, ta umurceta datana kai mata abinci tace injita, takira abdullahi da sufyan ta bukaci suje suga jikin yusuf din ko zaagane meke damunsa sun nufi fannin sa, suka tarar da likita ne sai bayi guda biyu, sufyan yazauna yadan duddubashi kasancewar yanada dan ilmi akan lafiya,yakuma tambayi likitan shidai likita yace jininsa tahau abinda yagani kenan, sufyan yadanyi dube dubensa sannan yaja gefe yazauna kusa da abdullahi yana cewa "nifa inaga akwai abunda ke damunsa yana boyena, its lyk akwai weak heart, mezai hana akaishi asibiti agani, abdullahi ya amince da shawaran, nan da nan ya umurci da azo akai yusuf asibiti , falmata wacce take fanninta tuni tafaso dakin hankali a tashe tana cewa " iiiiiina kuma zaku kaishi?" Daga yanda take jan maganan sufyan yagane cewa tabbas batada gaskiya, abdullahi yadaure fuska sannan yace "asibiti zamuje suduba jikin dakyau" "Babu inda zaku kaishi!" Cikin tsawa tafadi haka don saida hankalin bayin yakoma gun kowa ya tsaya jungum jungum, ganin basuda niyya yasa abdullahi yariko yusuf din dasauri sufyan yarikoshi alamun yabari karya rikoshi haka suka barshi akan gado suka fito domin kuwa falmata ta kasa ta tsare Bilki kuwa dataje kai abincin basu barta tashiga ba dole takoma tasanarwa yakolo abun yaci mata rai anma babu yadda ta iya dole ta san yadda zaayi a farkar yusuf kamin wani abu yasami aliya, sufyan kuma samu yayi ya lallabi abdullahi suka shiga gari babban asibiti suka dauko likita yazo da kayan aikinsa a fannin abdullahi yasauka wani daki da aka ware masa, suna jira dare tayi donsu cika aikinsu inhar basu magance matsalan adaren ba washegari zaa iya zartarwa aliya hukunci domin falmata tasa annemo hujjoji nacewa aliya mayyace kuma ita take illatashi inhar baakasheta ba yusuf bazai tashi daga sumbatun dayake ba,saida suka bari kafa yadauke sukaja likitan suka kaishi fannin yusuf suka rufo kofan, yayi bincike sosai yagano cewa kwaya aka bashi wacce tafi karfin kwalkwalwarshi hade da allura, saboda kasanceear aliya ce aransa yasa yake sumbatar sunanta, yadanyi dube dubensa sannan yace zaiyi alluran dazaiyi reversing dinshi, anmishi allurai kwaya biyu anma likitan yanuna musu cewa sai bayan awa hudu ko biyar yatashi hakan yasa dole suzauna agun, dukkansu babu wanda ya runtsa yusuf baitashiba sai hudu na asuba nan da nan suka lallaboshi yazauna suka watsa mai ruwa zai fara matsifa abdullahi yatoshe mai baki sannan yace yayi shiru yaji, cikin basira suka mai bayanin abunda ke faruwa sannan sukace hanya dayane don ceton aliya idan safiya tayi yacigaba da yadda yake inyaso idan antashi hukunta ta yafito yafadi gaskiya shikam tuni hankalinsa yatashi jin cewa aliya na cage saboda shi, zuciyarshi na radadi mikewa yayi waizaice yadaukota suka danneshi dakyar suka lallabashi ya yarda, kafinnan suka wuce fannin abdullahi don yin alwala sutafi masallaci alokacin ankira sallah Dasafe aliya idonta yacika ya kumbura ganin cewa yau komi zai iya faruwa da ita, taci kuka harta koshi ta godewa Allah,karfe goma saiga dogarai inda akaje da ita mahukunta, gurin da ake hukunta duk wanda yayi laifi acikin fada, ta sunkuyar dakanta ayayinda umma uwar soro taketa bayanin abubuwan da aliyan tadauka daga karshe tace "zaki fadi gaskiya ko ki fuskanci hukunci, ke ba baiwa bace da an miki hukunci mafi tsanani, sannan kinsan cewa hukuncin maita a masarautannan shine akashe mutum, donhaka kifadi gaskiya kisake yarima kisake kurwansa,donkar ki fuskanci tashin hankali, " Aliya kuka take sosai yayinda take kallon sufyan wanda ke mata alamun tayi shiru anma tagagara ganewa shikenan itakam yau mutuwa tazo mata, ta ina zata sake yusuf, gashi mintuna kadan aka bata tasakeshi, kukan datake harya hade zuciyanta alokacin. Kawai saiga yusuf yashigo filin falmata ita tafara tsorata tamike

To be continue....

Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.

No comments:

Post a Comment