Wednesday, 3 August 2016

Hallaccin Sarauta Episode 38

Continuation of Halaccin Sarauta 38

Reqd the previous episode HERE 

Aliya bata iya daga kai ba, tarasa meyake mata dadi, ayayinda falmata da yakolo ke magana, anma falmata tayi kif da ido tareda "cewa tunda ba danki bane saikiyi hakuri" yakolo taji zafin kalman dakinta takoma don abun yafi karfinta, Yusuf nafitowa daga masallaci yaga shehu wanda yayi latti, donsai alokacin zaishiga masalaccin [10/29, 7:10 PM] Adda Bena: Ganin yusuf yasa ya tarbesa tareda cewa

"kayi sauri kashiga ciki kaga ikon Allah hakan yasa yadada sauri jikinshi nabashi wani abu yafaru ne,aikuwa idonsa kan aliya yayi tana zaune a kasa , Allah sarki marainiyar Allah dasauri yaje yadauketa falmata nakiranshi bai kulataba fanninsu yanufa da aliya daki yakaita yaga babu bedshit nan da nan yagane me akayi mata ajiyeta yayi yaje yadauko kettle yahada mata ruwan zafi sannan yace "tashi kishiga," da taimakonsa tashiga bandakin tarufo, jin ta dade baikuma ji motsin ruwa ba yasa yabude bandakin tana zaune acikin bathtub din tana kuka, tausayinsa yakamata bata rai yayi sannan yace "zanmiki wankan" kallonshi tayi adan tsorace anma bai kulata ba, yarufo bayan gidan yakamota, tagara yimasa gaddama, haka yacire kayan yakunna showern kunya duk yarufeta, tagagara motsi haka yacudeta kaman jaririya sannan yadaukota ya ajiye, ya shafa mata mai yaciro mata kaya marar nauyi wani dogon riga ne haka, daya ciro yasamata, yahada mata tea a falo yazo yazauna ya lallabata tasha, itakam sai ganin ikon Allah take, mutumin datake masa kallon soko yau gashi soko na aikinsa,saida ya tabbatar batada matsala sannan yashiga yadau wanka, yafito fannin bayi yanufa, yasa akira masa wanda suka dauki aliya , sannan yafara fada akan me zasu taba mishi matarsa nemo dogarai yayi yasa aka basu jikinsu, saidaya tabbatar kowacce taji jiki sannan yanufi fannin yakolo yagaysheta anan tadada basa hakuri yanuna bakomi , yanufi gun falmata wacce tacika fam tana jiransa, zuwansa tafara masa fada akan me zai hukunta bayi sannan yafara gayda kishiyanta kafin ita, tunda tafara magana baice mata uffan ba harta gama,hakan yakara tunzurata tuni ta kullace aliya aranta, gani takeyi ta mallaka mata da, fitowarsa yanufi gun mahaifinsa suka fara gaysawa, kafin yakoma fanninsa, tare suka wuni har dare alokacin aliya tafarajin wannan kukan kuma, tuni tafara tsorata.

haka suka kara zama adaren basu runtsa ba, tuni aliya tafede rashin bacci yafara takurata. Ga ciwon kai ita saitana jinta asama itabaa kasa ba, baa sama ba, kaman jira kaman ana yawo da ita, Ga rashin kwanciyan hankali haka suka jera sati ahaka bata bacci daredare dasafe kuma inta kwanta saitahau mafarki,ganin abun banayi bane yasa yusuf yakira sufyan suka gayamasa abunda yafaru tunda yake baitaba shiga tashin hankalin ba, nan yafara dana sanin amince mata ta auri yusuf, bai kawo kowa aransa ba anma yasan akwai wanda basuson aliya da yusuf, akwai wani malamin da sufyan yasani donhaka ya umurci yusuf da aliya suje gunshi, Babban malami ne yanada almajirai nan yusuf yabukaci ganinsa, aka musu iso a zaure, malamin yashigo , aliya sanye takeda babban gyale yarufe fuskanta hannunta ne kawai awaje, malamin nazama, yace "subhanallah, ciro abun hannunki" dasauri tafara ciro zobunan, yace "a a.

Na azurfan" cirowa tayi tamika masa, yakarba dasauri ya kira almajiri daya yamika masa sannan yace yaje ya sa awuta, sannan yajuyo yakalli aliya tareda cewa "baiwar Allah kinata yawo da tsafi ajikinki, ai kurwanki ake yawo dashi asama, " tuni jikinta yafara bari, yusuf yakalleta tareda cewa "waya baki zoben?" "Acikin kayan aurena nagani" baice komi ba inda malamin yace sutafi meke tafe dasu, tamishi bayani zalla zallah Yace "dafarko jirin dakikeji wannan zoben ne, shiyake jawo haka yawo ake da kurwanki asama,, nabiyu kuma asiri ne akamaki mai suna janduks, shi wannan sihiri anayine wa mutum inda mutum zaisa ranshi a tsaka," daga yusuf har aliya gyra zama sukayi don kowannensu yagama tsorata jikinsu na bari, musamman aliya, duk dabarun sihiri data karanta bata karanto dawannan ba, "Sihiri ne akewa mutum na kwana ashirin, dafarko akan dauki hoton mutum kowani abu dakika mallaka a yi amfani dashi, sannan wannan sihiri shine zakina jin kukan dabobbin dakikafi tsoro, inkin kwanta kuma zakina mafarkin kura, shiwannan kura zaina binki ne,har kwana ashirin idan kuran ta yakeki zaki mutu acikin kwana ashirin, idan kuma ke kika yaketa zata koma kan wnda yayi sihirin, kinada wani tabo ajikinki dakika samu a mafarkin?" Ta gyada kai tareda cewa "kuran danake mafarkinsa kullum inna tashi sainaga cizon ajikina yayi baki". Yace "haka sihirin take, yanzu zanbaki dabarun karyawa, inbaki karyaba zaki iya rasa ranki Allah ya sauwaka" aliya da yusuf jikinsu na bari sukace to inda yaci gaba da bayani yana cewa "Akofar dakinki ko kuma tsakar gydanki kinemi rami akwai inda aka birne laya kiduba, dole sai an birne laya medauke dasunan wanda akeso ya mutu din,

kinemo acire, sannan inzakiyi bacci kikaranta yasin, fatiha, falaq, nas, da suratul jinni, kikaranta kikwanta zakiyi mafarki anma zakisamu karfin yakanta, donhaka kisamu ki kashe wannan kuran hakan kadai zaisa kizauna lafiya, sannan dalilin ganin wannan kuran wanda yayi asirin kowani dare yana kona laya da takarda me dauke da sunanki donhaka saiki dage da addua wani lokacin mune bama nemawa kanmu tsari, munsan sihiri nakama mutum anma zamu iya karyawa,ki kasance kina bacci da alwala, ki kasance kin rike hisnul muslim,ki guji zama cikin najasa, Allah yana taimakawa wanda ya taimakawa kansa ne" Sunmasa godiya sosai sannan suka mike sukafito dakyar aliya take tafiya jin ance kwana ashirin, acikin kwana ashirin taci bakwai, ashe dama haka abdullahi yaji daya bata kodanta yasan zai iya mutuwa kowani lokaci, ashe haka yaji? Innalilah kuka tafarayi yusuf harya tukata gyda. Sannan yafara lallabinta, dakyar tashanye kukan tafito bilkisu takira tareda cewa tanemo dogarai, suna isowa tafito itama tace sufara tone gun duk inda sukaga laya kowani abu na alajabi su kawo, tana tsaye akansu tana jira nima benaxiratu nadau gatari daya nafara dube dube don naga kozan samu.

To be continue....

Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.

No comments:

Post a Comment