Wednesday, 18 April 2018

Kotu Za Ta Bayyana Ranar Da Za A Bayyana Kudaden Da Aka Kashe Wajen Jinyar Buhari


Wata kotun tarayya ta sanya ranar 5 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan karar da kungiyar ASRADI ta shigar bayan da Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele ya ki amincewa da bukatar kungiyar na bayyana mata adadin kudaden da aka salwantar wajen jinyar Shugaba Buhari a London.


Tun da farko ne dai, Shugaban Kungiyar ta ASRADI, Chukwuwike Okafor ya shaidawa Alkalin kotun, Mai Shari'a John Tsoho cewa sun gabatar da wannan bukata na neman sanin kudaden jinyar ce karkashin dokar 'yancin sanin bayanan gwamnati amma kuma Shugaban Bankin ya yi fatali da bukatar ta su


Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment