Thursday, 19 April 2018

An Gano Sandar Iko Na Majalisar Dattawa Da Aka Sace


Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa ta gano sandan iko na majalisar Dattawa wadda wasu 'yan daba suka sace a lokacin zaman majalisar a jiya Laraba.


A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar 'yan sandan ta nuna cewa ta gano sandar ce a karkashin gadar da ke kusa City Gate a cikin birnin Abuja wanda a nan ne 'yan dabar suka jefar da ita. Sanarwar ta ci gaba da cewa a halin yanzu rundunar ta dukufa wajen cafko wadanda suka aikata laifin.


Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment