Wednesday, 18 April 2018

'Yan Daba Sun Arce Da Sandan Iko Na Majalisar Dattawa


Wasu 'yan daba da suka yi ikirarin suna tare da dan majalisar Dattawan da aka dakatar, Sanata Ovie Omo-Agege sun kutsa kai zauren majalisar inda suka arce da sandan ikon majalisar.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan dabar wanda sun kai su goma sun iso harabar majalisar ce Jin kadan bayan isowar dakataccen dan majalisar inda suka shaidawa masu gadin zauren majalisar cewa suna tare da Sanatan ne wanda suka kuma arce da sandan ikon majalisar.

Wadanda abin ya auku a kan idonsu sun bayyana cewa 'yan dabar sun shiga zauren majalisar ce a daidai lokacin da Mataimakin Shugaban Majalisar, Ike Ekwuremadu ke jagorantar zaman majalisar. A makon da ya gabata ne dai, Majalisar ta dakatar da Sanata Ovie Agege bisa nuna adawa da matakin da majalisar ta dauka na canja ranar zaben Shugaban kasa. Ita dai wannan sandar sai da ita ce kawai za a iya zaman majalisar
Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment