Thursday, 19 April 2018

Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Cin Zarafin Mutane Masu Mutunci A Kafafun Sadarwa, Inji Rundunar 'Yan Sandan Kano


Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce za ta sanya kafar wando daya da ma'abota shafukan sada zumunta wadanda suke cin mutumcin jama'a da yin kalaman tayar da tinziri.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Majia, yace rundunar ta shirya tsaf wajen magance wannan matsala, inda ya ce sam ba daidai bane wasu tsirari su ringa amfani da wannan kafa wajen yin batanci ga masu mutunci ba, yace wasu na amfani da wannan kafa wajen zagin malaman addini da shugabanni ta hanyar hada hotunan su da matan banza ko dabbobi da yin zantukan da basu kamata ba.


SP Majia , ya kara da cewa rundunar zata samar da kwararrun jami'anta da suka iya amfani da wadannan kafafen sada zumunta na zamani tare da basu duk abinda ya kamata domin subi sahu da gano masu aikata wannan mummunar dabi'a ta zagi, cin mutumci da wulakanta al'umma.
Yace duk wanda aka za'a dauki matakin ladabtarwa akan shi, ko dai aja masa kunne tare da gargadi, ko kuma a gurfanar da ko waye a gaban kotu.Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment