Thursday 19 April 2018

Gwamnatin Jihar Kaduna Za Ta Kara Daukar Malaman Firamare Guda Dubu 13,665




Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa'i, ta shirya tsaf domin sake daukar kwararrun Malaman Firamare 13,665, a wani shiri na kara inganta harkar ilimi a fadin jihar.
Kwamishinan Ma'aikatar ilimi ta Jihar Alhaji Ja'afaru Sani ya bayyana hakan, a yayin wani taron manema labarai da Ma'aikatar ta kira a ranar Larabar nan.

Kwamishina Ja'afaru Sani ya cigaba da cewar, tuni hukumar bada ilimin bai daya ta Jihar ta dauki Malamai 11,335, domin cike gibin Malamai 25,000 da Gwamnatin Jihar ta sallama biyo bayan rashin kwarewa.
Malamai 25,000 da za'a dauka zasu maye gurbin 22,000 wadanda suka gagara cin jarrabawar da Gwamnatin Jihar tayi musu.
Kwamishinan Ma'aikatar ilimin ya kara da cewar Mutum 40,000 ne suka zauna zana jarrabawar daukar Malaman, inda aka kira 27,639 domin ganawa da su, Mutum 15,897 daga cikin wadanda suka zana jarrabawar sun samu nasara, inda a tantancewa ta gaba aka sake rage wadanda aka shigo da sunayen su ta bayan gida.
Ja'afaru Sani ya cigaba da cewar bayan kammala tantancewar gaba daya, Mutum 4,562 wadanda aka shigo da sunayen su ta hanyar da bata dace ba, akayi fatali da su inda aka bar ainihin Mutum 11,335 wadanda suka cancanta, cikin wadannan adadi na 11,335 wadanda suke da shaidar karatu ta Digirin Digirgir an aike dasu Makarantu Firamare 4000 domin cigaba da karantarwa.
Kwamishinan ya cigaba da cewar an kara karbar takardar neman aikin daukar Malaman domin cike gibin 13,665, sannan tsarin daukar Malaman na tafe ne akan ka'ida wacce Gwamnatin Jihar ta gindaya.
"Muna fatan za mu kammala daukar Malaman kafin nan da karshen watan Mayu na shekarar da muke ciki, sannan Gwamnati na wani shiri na ganin an sanya ilimin kimiyya a Manhajin Makarantun Sakandare mallakin Gwamnatin Jihar.



Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment