Tuesday 12 June 2018

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato

Hukumar Yan sanda reshen Jihar Sakkwato ta tabbatar da rasuwar mutane takwas a wata rikici da ya barke tsakanin yan baranda da yan banga a jiya Litinin a karamar hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, Cordelia Nwawe ta shaidawa yan jaridar cewa ana kyautata zaton mutane takwas ne suka rasu ciki har da wani dattijo da yan barandan su kayi kokarin sacewa.

Mrs.Nwawe ta kara da cewa har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin, ta kuma ce ana kyautata zaton yan barandan sun zo ne daga kauyukan jihar Zamfara da ke makwabtaka da Sakkwato.

Ta kuma ce kwamishinan Yan sanda na jihar ya ziyarci kauyen da abin ya faru don yin jaje ga iyalen wadanda abin ya shafa tare da tabbatar musu cewa yan sanda za su binciko wadanda suka aikata wannan laifin.

Sai dai a wani rahoton, an ce mutane 13 ne suka rasu sakamakon yunkurin da yan barandan su kayi na sace wani dattijo ranar Asabar a kauyen Dan Tasango a Gundumar Gebe.

A cewar wani ganau, yan barandan sun harbe dattijon ne saboda ya ki yarda su tafi dashi, hakan ne yasa yan bangan garin suka hada kai don bin sahun yan barandan.

Majiyar ta cigaba da cewa 'yan barandan sunyi wa yan bangan kwantar bauna a hanyar Kamarawa-Barafawa inda akayi musayar wuta inda yan barandan suka kashe yan banga bakwai su kuma aka kashe musu mutane biyar.

Sai dai yan barandan sun kwace gawawwakin mutane biyar din da aka kashe musu kamar yadda suka saba saboda kar a gane kosu wanene.

No comments:

Post a Comment