Saturday, 12 May 2018

Dubunsa Ta Cika Bayan Ya Je Sata A Babban Asibitin Jihar Kaduna Amma Kofa Ta Ki Buduwa

Dubun wani barawo da yake shiga  dakunan masu jinya dake babban asibitin jihar Kaduna na Yusif Dan Tsoho da aka fi sani da Asibitin Dutse yana dauke-dauke ta cika.

An dai kama shi ne bayan ya yi shigar burtu ya shiga bangaren maza, inda  ya yi kamar yana jinyar wani ne, inda bayan kowa ya yi barci ya bi ya kwashe musu wayoyi.

Saidai bayan kwashe wayoyin ne asirin sa ya tuno, bayan ta tarar da kofar sashin a kulle kamar yadda aka saba idan dare ya yi ana kulle duk  kofofin sashi na asibitin.

Yanzu haka dai dukkan wandanda ya satarwa wayoyin sun karbi kayansu, sannan suka damka shi ga jami'an tsaron dake kula da asibitin domin ci gaba da bincikarsa.

No comments:

Post a Comment