Thursday, 3 May 2018

Masarauta Dutse Ta Tsige Mustapha Sule Lamido A Matsayin Hakimin Bamaina

Masarautar Dutse Karkashin Jagorancin Mai Martaba Sarkin Dutse, Alh  Nuhu Muhammadu Sunusi, Ta Tsige Mustapha Sule Lamido Daga Matsayinsa Na Sarautar Hakimin Dutse Sabo Da Wasu Dalilai.

Tun Farko Dai Masarautar Dutse Ce Ta Takaddar Da Mustapha Sule Lamido Daga Sarautar Shi, Bayan Da Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Shigar Da Takkaddar Koke Akan Shiga Harkokin Siyasa Da Yakeyi A Matsayinsa Na Hakimi Mai Kasa.

Tuni Masarautar Dutse Ta Tura Sabon Hakimi Wanda Zai ci gaba Da Kula Da Yankin Bamaina A Matsayin Sabon Hakimi.

Sai Dai Masarautar Ta Dutse Ta ce Mustapha Sule Lamido Zai Iya Ci gaba Da Amfani Da Sunan shi Na Sarautar San Turaki.

Dama Dai An Nada Mustapha Sule Lamido Ne A Matsayin Hakimin Bamaina A Lokacin Mulkin Sule Lamido.

No comments:

Post a Comment