Friday, 18 May 2018

Kotu ta dage shari’ar Sanata Dino Melaye har sai baba ta gani

Wata babbar kotun birnin tarayya a ranar Alhamis ta daga sauraron shari’ar Sanata Dino Melaye na jihar Kogi, dagawar da babu wani lokacin sake zama tabbatacce sakamakon matsalar rashin lafiyarsa.

Hukumar ‘Yan Sanda tana karar Sanata Melaye ne a birnin tarayya da kuma garin Lokoja, inda a birnin tarayya suke zarginsa da yunkurin kashe kansa da kuma bata kayan gwamnati, wanda sanadiyar haka aka kwantar da shi a asibiti.

A garin Lokoja kuma ‘Yan Sandan na tuhumarsa da laifin yiwa hukumar karya da kuma bawa ‘yan ta’adda makamai.

Alkalin na birnin tarayya Olasunbo Goodluck, ya bukaci Lauyan wanda ake kara, Rickey Tarfa, ya bayar da kwakkwaran bayani game da rashin bayyanar Melaye a gaban kotun a ranar Laraba, inda ya gabatar da takardunsa na asibiti a gaban kotun.

Sakamakon haka kotun ta gamsu da cewa Mr. Melaye, yana kwance a asibiti bangaren wadanda ake bawa kulawa ta musamman, wanda dalilin hakan ne Alkalin kotun Goodluck ya daga shari’ar dagawa ta har sai baba ta gani.

No comments:

Post a Comment