Friday, 4 May 2018

Jagoran siyasar jihar Gombe ya kaddamar da motocin daukar marassa lafiya.

Da safiyar yau Mai girma jagoran siyasar jihar Gombe Sanata Danjuma Goje, ya kaddamar da Sabin motocin daukar marrasa lafiya Guda 5 ga asibitoci Daka yankin Gombe ta'tsaya.

Motocin da aka raba Guda biyar, an rabasu ne ga asibitocin Zambuk, Hinna, Deba, Kalshingi, Kumo, da Akko gari.

Cikin jawabinsa yayin mika motocin ga al'ummar yankin Gombe ta'tsakiya sanata Danjuma Goje yace irin wadannan motoci ya rabasu a lokacin da yake Gwamna jiha, kasan cewar yadda motocin suka lalace yasa ya kawo sabi don rabasu ga asibitocin yankin Gombe ta'tsakiya.

Muhammad Adamu Yayari
05-04-2018

No comments:

Post a Comment