Friday, 4 May 2018

PDP Za Ta Kwace Jihohi 27 Daga APC A Zaben 2019 — Atiku


Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa jam'iyyar PDP za ta kwato akalla jihohi 27 daga jam'iyyar APC a zaben 2019 yana mai cewa al'ummar Najeriya sun dawo rakiyar APC .

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce gwamnatin APC ta jefa 'yan Najeriya cikin yanayin kuncin rayuwa inda ya jaddada cewa shugabannin dake mulkin kasar a yanzu, ba su taka rawa wajen gwagwarmayar ganin tsarin dimokradiyya ya samu gindin zama a Najeriya ba.

No comments:

Post a Comment