Friday, 18 May 2018

Kwankwaso ba zai iya hana shugaba Buhari cin kano ba – Inji El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi ba'a da shagube ga wasu kusoshin jam'iyyar APC dake barazanar barin jam'iyyar, inda yace barin jam'iyyar tasu bazai hana Shugaban kasa Muhammadu Buhari lashe zabe ba a 2019.

A kwanakin baya dai wasu manyan 'yan siyasa wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a 2014, suka yi zargin cewa an mayar dasu saniyar ware tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya musu bukatunsu ba.

Sai dai Gwamna E-Rufa'i ya yi masu hannunka mai sanda inda yace barinsu jam’iyyar ba zai hana shugaban kasar kawo jihohinsu a 2019 ba.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata, El-Rufai, ya ce"tun shekarar 2003 shugaban ke lashe zabe a Kano."Ya cigaba da cewa idan aka yi duba ga yawan mutanen da suka fito saboda tarban Buhari, za a ga cewa Kano wuri ne da shugaban ya ke da magoya baya sosai
Ya kuma ce, wannan gangamin taro ya faru ne ba tare da jama'ar Kwankwaso ba.

No comments:

Post a Comment