Sunday 27 May 2018

Shehu Sani da Hunkuyi suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC, dalilansu...

Wani bangare na jam'iyyar APC da ke karkashin jagorancin Sanata Suleiman Hunkuyi da ke wakiltar Kaduna ta arewa da Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya sun ce akwai yiwuwar za su fice daga jam'iyyar.

A wata sanarwa da suka fitar a jiya Juma'a, sanatocin biyu da ke kiran kansu da suna APC Akida sunce sun kammala bita akan jam'iyyar da matsalolin shugabancin da ke adabar jam'iyyar a jiha da ma kasa kuma suna tunanin ficewa daga jam'iyyar da suka taimaka wajan kafawa.

APC Akida ta ce za ta dauki matakin ficewa ne "Idan babu wata kwakwarar alamar samun nasara wajen magance matsalolin wariyar da kuntatawa da ake yiwa wasu yan jam'iyyar a jihar Kaduna"

Shugaban kungiyar, Tom Maiyashi, wanda ya fitar da sanarwar ya ce akwai wasu abubuwa guda biyu da suka faru a jihar wanda suka tabbatar masa da cewa babu shugabanci na gari a jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna kamar yadda The Cable ta rawaito.

"Yadda aka gudanar da zabukan shugabanin jam'iyya da kuma zabukan kananan hukumomi a jihar ya tabbatar min da cewa rashin jagoranci mai kyau zai dushe duk wani farin jini da jam'iyyar ke dashi a jihar."

Dama dai kungiyar APC Akida ta bayyana yiwuwar faruwar hakan tun da fari lokacin da ta lura da irin kamun ludayin gwamna Nasir El-Rufai," a cewar Maiyashi.

A saboda wannan dalilan ne kungiyar ke kira ga duk wadanda gwamna El-Rufai ke ganin girmansu da su hanzarta jan kunnensa domin kare jam'iyyar daga fadawa cikin bala'i.

Kungiyar kuma ta sanar da mahukuntan jam'iyyar a jiha da kasa cewa za su fice daga jam'iyyar idan har ba'a yi gyara ba.

No comments:

Post a Comment